Birnin Hatra na da tazarar kilomita 70 daga garin Mosul na Iraki a kudu maso yamma, wanda ya taba zama muhimmin sansanin soja na daular Parthia da hedkwatar daular Larabawa ta farko. A shekarar 1985, kungiyar UNESCO ta sanya shi cikin jerin sunayen kayayyakin tarihin duniya.
A jiya Asabar 7 ga wata, gwamnatin Iraki ta ba da sanarwar yin Allah wadai da kungiyar IS da ta lalata tsohon birnin Hatra dake cikin jerin kayayyakin tarihin duniya.
A wannan rana kuma, hukumar yawon shakatawa da kayan tarihi ta Iraki ta ba da sanarwar cewa, 'yan kungiyar IS sun sace kayayyakin tarihi masu daraja na tsohon birnin Hatra, tare da lalata birnin.
Kungiyar UNESCO ta ba da sanarwar cewa, kungiyar IS ta aikata laifin yaki a sakamakon lalata kayan tarihi da gangan, yayin da babban sakataren MDD Ban Ki-moon shi ma ya soki wannan danyen aiki da babbar murya, inda ya ce, kungiyar ta aikata laifin yaki sakamakon yadda ta lalata kayayyakin tarihi na dan Adam baki daya, hari ne da ta kai wa duk bil'adam.(Fatima)