in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin kasar ta Iraqi ta amince da manyan jami'an kasar da aka nada
2014-10-19 16:53:40 cri

Majalisar dokokin kasar ta Iraqi ta kira wani taro a ran 18 ga wata, inda ta zartas da sunayen 'yan takara da firaministan kasar Iraqi Haider al-Abadi ya gabatar kan mukaman ministan harkokin cikin gida da na tsaron kasar da dai sauran manyan mukaman da ba a nada kowa ba.

Mambobin 261 daga cikin 328 na majalisar sun halarci taron, inda suka kada kuri'u da zartas da wannan takardar sunayen da Haider al-Abadi ya gabatar. Bisa wannan takarda, dan takarar darikar Shi'a Mohammed Salim al-Ghabban da dan takarar darikar Sunni Khalid al-Obiedi za su rike mukamin ministan harkokin cikin gida da ministan tsaron kasar.

Bisa kuri'un da aka jefa, Roj Nuri Shawis zai ci gaba da rike mukaminsa na mataimakin firaministan kasar, kuma mataimakin firaministan kasar mai ci Hoshyar Zebari zai canja mukaminsa zuwa ministan kudin kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China