Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin tana maraba sosai da kafa sabuwar gwamnati a kasar Iraqi, wannan wani babban ci gaba ne da aka samu a kokarin da ake yi na warware takaddamar siyasar kasar, kasar Sin na fatan bangarorin kasar Iraqi da abin ya shafa za su ci gaba da karfafa hadin gwiwar a tsakaninsu, don ciyar da yunkurin neman sulhu ta hanyar siyasa da farfado da tattalin arzikin kasar gaba, ta yadda za a iya shimfida zaman lafiya da tsaro a duk fadin kasar cikin sauri, tare da samar da dauwamammen ci gaba a kasar.
Haka kuma, kasar Sin tana son ci gaba da taimakawa kasar Iraqi a lokacin da bukatar hakan taso yadda ya kamata.(Maryam)