Rahotanni daga bangaren sojan kasar Iraki na cewa, sojojin tsaron kasar da dakarun fararen hula na kungiyar Shi'a sun kai hari tsakiyar birnin Tikrit, inda suka kwace arewacin birnin, yankin masana'antu da ke yammacin birnin da kuma asibitin dake kudancin birnin da sauran muhimman wurare.
Jagoran sojojin gwamnatin kasar Iraki yana ganin cewa, ci gaban da aka samu a halin yanzu ya dace da hasashen da aka yi, kuma yanzu haka sojojin gwamnatin kasar suna ci gaba da yin musayar wuta da dakarun kungiyar IS a kokarin kwace yankin kudancin birnin Tikrit.
Sai dai, sojojin gwamnatin kasar ba su kwace fadar tsohon shugaban kasar Saddam Hussein dake birnin ba. (Zainab)