Jami'in ya ce dakarun kawancen kasa da kasan sun samu bayanan sirri, sa'an nan suka kai farmaki ga mayakan da ke garin Al-Qa'im, da maboyar wasu manyan jami'an kungiyar IS, wanda hakan ya haddasa mutuwar dakarun kungiyar IS a kalla 15, tare da jikkata wasu fiye da 30.
Wani jami'in na daban a hukumar tsaron kasar Irakin ya bayyana cewa, sojojin kasarsa za su kaddamar da ayyukan soja a jihar Salahudin dake arewacin kasar cikin awoyi 72 masu zuwa, don murkushe dakarun kungiyar IS dake jihar. (Zainab)