in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashewar boma-bomai sun haddasa rasuwar mutane da dama a Yemen
2015-03-21 17:18:20 cri

Jiya Jumma'a 20 ga wata, an kai hare-hare a wasu masallatai da hukumomin gwamnati na kasar Yemen, inda aka ji fashewar boma-bomai da dama, kuma bisa labarin da hukumar tsaron kasar ta bayar, an ce, ya zuwa yanzu, mutane 159 sun rasa rayukansu a sanadiyyar fashewar boma-bomai, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Kuma ma'aikatar harkokin wajen kasar Saudi Arabia ta sanar a ran 20 ga wata cewa, kasar za ta aike da kayayyakin agaji zuwa kasar Yemen, domin ba da jinya ga wadanda suka jikkata sakamakon hare-haren boma-bomai da rikice-rikicen da suka barke a kasar.

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa ta bakin kakakinsa a jiya Jumma'a, inda ya yi allawadai da hare-haren da aka kai a kasar Yemen, wadanda suka haddasa rasuwa da jikkatar mutane da dama. Kuma sanarwar ta cigaba da cewa, ya kamata bangarorin da abin ya shafa na kasar Yemen su cika alkawarinsu na warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar zaman lafiya, da kuma shigar shawarwarin da MDD ta shirya da kuma cimma matsayi daya kan dabarar warware matsalar bisa takardu, yarjejeniyoyin da abin ya shafa.

A nasa bangare, kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwa cewa, ya yi allah wadai da hare-haren boma-bomai da aka kai a babban birnin kasar Yemen, Sanaa da lardin Sadah, wadanda suka haddasa rasuwa da jikkatar mutane da dama, tare da jaddada cewa, ya kamata a yaki da dukkanin irin ta'addanci.

Jiya Jumma'a 20 ga wata, kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin hare-haren Yemen, kana ta ce, za ta ci gaba da kai hare-hare ga kungiyar Houthi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China