in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani hari a hedkwatar Iraki ya halaka mutane 41
2014-10-12 16:44:36 cri

Hukumar tsaron kasar Iraqi ta ba da labari a ran 11 ga wata cewa, an kai harin kunar bakin wake na mota sau biyu a Baghdad, babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 41, yayin da wasu 75 suka jikkata.

An ba da labari cewa, an kai wani harin kunar bakin wake na mota a yankin Shuala dake arewa maso yammacin birnin, wurin dake cike da fararen hula, lamarin ya hadasa mutuwar mazauna wurin 28 yayin da wasu 40 suka ji rauni tare da lalata gidaje da dama dake kewayen wurin.

Daga baya kuma, an kai irin wannan harin a yankin Kadhimiya dake arewacin birnin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 13, yayin da wasu 35 suka raunuka.

Tun farkon wannan shekara da muke ciki, aka rika kai hare-hare da ayyukan ta'addanci a kasar ta Iraqi, lamarin dake kara sanya Iraqi cikin mawuyacin hali.

Bisa kididdigar da hukumomin MDD suka bayar, an ce, tun farkon wannan shekara da muke ciki, yawan mutane da suka mutu sakamakon hare-hare da ayyukan ta'addanci da aka gudanar a kasar ta Iraqi ya kai 5500, yayin da wasu fiye da dubu 11 suka raunuka. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China