in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Iraqi ya bukaci gamayyar kasa da kasa da su hada gwiwa wajen yaki da ta'addanci
2014-11-30 17:07:08 cri
Mataimakin shugaban kasar Iraqi Nouri al-Maliki wanda ke ziyarar aiki a kasar Lebanon a yanzu haka, ya bukaci gamayyar kasa da kasa da su dauki matakan hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci.

Nouri al-Maliki ya bayyana haka ne ga kafofin watsa labaru, jim kadan da saukarsa a filin jirgin birnin Beirut, fadar gwamnatin kasar ta Lebanon.

Mr. Maliki ya ce, ya kamata a zage damtse wajen ganin-bayan kungiyar IS ba kawai a kasar Iraqi ba, har ma da sassan kasar Syria, duba da kusancin kasashen biyu, da ma tarihi makamanci dake tsakanin su.

Ya ce kamata ya yi gamayyar kasashen duniya, su dauki matakan bai daya cikin hadin gwiwa kan wannan muhimmin aiki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China