in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mamban majalisar gudanarwar Sin Yang Jiechi ya ziyarci Iraqi
2015-03-23 15:09:23 cri
Bisa goron gayyata daga gwamnatin Iraqi, mamban majalisar gudanarwar Sin Yang Jiechi ya ziyarci Iraqi, kuma ya gana da shugaban kasar Fouad Massoum, da sauran shugabannin kasar a birnin Bagadaza hedkwatar kasar.

Mr. Yang ya ce, Sin ta dora muhimmanci sosai game da huldar hadin gwiwa ta sada zumunta tsakaninta da kasar Iraqi, kuma yana fatan inganta mu'amala da manyan jami'an kasar, don kara amincewa juna a fannin siyasa, da yalwata hakikanin hadin gwiwa, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, don daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Shugaban kasar Iraqi ya bayyana cewa, Iraqi ta yaba wa ci gaban da Sin ta samu, kuma ta jinjina matsayin adalci da Sin ke tsayawa kan sa, wajen daidaita batutuwan duniya, tana kuma godiya ga goyon baya da Sin ke nuna game da sha'anin samar da tsaro da karko a kasar.

Ya ce Iraqi na dora muhimmanci game da alakar da ke tsakaninta da Sin, kana tana fatan inganta hadin gwiwa a fannonin makamashi, da sadarwa, da aikin gona, da kimiyya da fasaha, don sa kaimi ga mu'amalar sada zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China