Tuni dai shugaba Obama ya mika kudurin neman amincewar majalisar dokokin kasarsa, na neman izinin amfani da karfin soja wajen yaki da kungiyar ta IS.
Minista Carter ya bayyana hakan ne a jiya Laraba yayin da yake halartar taron sauraron ra'ayoyin jama'a, game da shirin na shugaba Obama na neman samun izinin amfani da karfin soja a yakin da ake yi da IS, wanda kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattijan Amurka ya gudanar.
Carter ya kara da cewa koda yake lokacin da Obama ya kayyade karkashin shirinsa, wato shekaru uku ya dace da halin da ake ciki, amma babu tabbas na cimma wannan buri a cikin wannan wa'adi.
Ban da wannan, Carter ya ce dalilin da ya sa shugaba Obama ya gabatar da shirin yaki da kungiyar IS cikin shekaru uku masu zuwa, shi ne domin baiwa jama'ar kasar damar bincikar sakamakon da za a samu a wannan aiki, tare da samar da ma'aunin nasarar hakan, ga sabbin shugabannin majalisar dokokin kasar da za a zaba a karo mai zuwa, wanda hakan zai taimaka musu wajen tsara kudurin ci gaba da wannan shiri ko kuma akasin hakan. (Zainab)