Ministan harkokin wajen kasar Sin Mr Wang Yi a zantawar sa da manema labaru kafin kammala taron ministocin harkokin wajen kasa da kasa kan batun nukiliyar Iran a daren talatan nan, inda ya bayyana matsayin Sin kan wannan batu dake kunshe da bangarori hudu. Na farko, ya ce a nace ga ba da jagoranci irin na siyasa wato ta hanyar yin shawarwari, na biyu kuma, a hada gwiwa tsakanin bangarorin daban-daban don kai ga matsaya daya, sannan na uku, a cimma matsaya daya bisa matakai-matakai da samo bakin zare, sannan kuma na hudu, a warware duk matsalolin gaba daya ba tare da bata lokaci ba.
Mr Wang ya kara da cewa, a cikin shekara daya da ta gabata, Sin ta taba gabatar da wasu shawarwari masu amfani, sannan kuma a kokarin da take yi ta nuna himma da gwazo don shiga tsakani. Ban da haka, a cikin taron da aka yi a wannan rana, Sin ta gabatar da tunaninta na warware rikici yayin da ake fuskantar mawuyacin hali, matakin da zai ba da gudunmawa wajen cimma wata yarjejeniyar a dukkan fannoni. (Amina)