in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan Amurka da na Iran sun ci gaba da ganawa game da batun nukiliyar kasar Iran
2015-03-18 13:56:06 cri
Wata sanarwar da tawagar Amurka dake birnin Geneva ta fitar a jiya Talata, ta ce sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, da ministan harkokin wajen kasar Iran Javad Zarif, sun ci gaba da gudanar da shawarwari game da batun nukiliyar kasar Iran.

Taron na birnin Lausanne dake kasar Switzerland ya samu halartar ministan harkokin makamashi na kasar Amurka Ernest Moniz, da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran Ali-Akbar Salehi, da kuma wasu manyan jami'ai da dama.

Sai dai sanarwar ba ta yi karin haske game da sauran batutuwan da aka tattauna a yayin shawarwarin ba.

A jawabin sa yayin zaman tattaunawar, shugaban hukumar makamashin nukiliyar kasar ta Iran Ali-Akbar Salehi ya ce, Amurka da Iran sun riga sun warware yawancin manyan matsalolin da suka jibanci batun nukiliyar kasar ta Iran, kuma za su ci gaba da kokarin warware sauran matsalolin da suka rage a nan gaba.

Bisa wani labarin da kamfanin dillancin labarun kasar Iran FNA ya fitar, an ce bayan kammalar shawarwari tsakanin Salehi da Moniz, wakilin na Iran ya yi albishir da warware kusan kaso 90 cikin dari na matsalolin da suka shafi fasahohi, inda ya ce yanzu haka sauran matsala daya tak, a kaiga warware dukkanin batutuwan da ake takaddama a kan su.

Wakilan kasashen shida da batun nukiliyar ya shafa, wato Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Rasha, da Sin, da Jamus da kuma na kasar Iran, za su gudanar da shawarwari a zagaye na gaba, a ranar 18 ga watan nan a birnin Lausanne, inda ake sa ran shugaban sashen kula da kayyade makaman soja, na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Qun, zai jagoranci wata tawaga da za ta halarci shawarwarin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China