A yau ne, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da ministan harkokin wajen kasar Iran Javad Zarif suka yi shawarwari a birnin Lausanne na kasar Switzerland, inda suka yi kokarin ci gaba da kawar da sabani da zummar cimma wata yarjejeniya kafin karshen wannan wata.
A wani shirin gidan talabijin na CBS na Amurka, mista Kerry ya ce, idan Iran ta tabbatar da cewa, za ta yi amfani da makaman nukiliya ne domin wanzar da zaman lafiya, to, watakila za a cimma wata yarjejeniyar siyasa ta wucin gadi nan da 'yan kwanaki masu zuwa.
Sa'an nan, a jiya Lahadi kafofin yada labaru na Iran sun ruwaito mista Zarif na cewa, idan kasashe 6 da batun nukiliyar Iran ya shafa sun bayyana fatansu na cimma yarjejeniya a siyasance kamar yadda Iran take yi, to, za a cimma wata yarjejeniya. (Tasallah Yuan)