Netanyahu ya bayyana hakan ne a gaban 'yan majalisar dokokin kasar Amurka, yana mai cewa yarjejeniyar da ake shirin amincewa sam bata da dace ba.
Ya ce yarjejeniyar ta amince da kasar Iran da ta kiyaye na'urorin samar da makamashin nukiliya, ta yadda za ta iya samun isassun kayayyakin da take bukata don kera makaman nukiliya cikin gajeren lokaci, don haka a ganin sa yarjejeniyar rahusa ce ga kasar Iran.
Bayan jawabin na firaminista Netanyahu, shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana cewa, Netanyahu bai gabatar da shirin da zai iya maye gurbin yarjejeniyar batun nukiliyar kasar Iran, da watakila za a amince da ita ba.
A wani ci gaban kuma, game da jawabin Netanyahu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Marziyeh Afkham, ta ce jawabin Netanyahu wani wasan kwaikwayo ne na aringizon kalamai, wanda ke kunshe da sakon masu tsattsauran ra'ayi dake Tel Aviv, gabanin zaben shugaban kasar dake tafe. (Zainab)