Bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasar Iran da wadannan kasashe 6 wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin, da Jamus, a watan Nuwamban shekarar 2013, an ce, Iran ta amince da daukar matakai masu sassauci wajen raya shirinta na nukiliya, a nasu bangaren kuma kasashen yammacin duniya za su yi sassauci wajen kakaba mata takunkumi, kuma a tsakiyar shekarar 2014, bangarorin daban daban za su yi shawarwari don cimma wata yarjejeniya a dukkan fannoni. Amma, sabo da bambanci a tsakaninsu, bangarorin daban-daban sun dage shawarwarin zuwa watan Nuwamba na bara, daga baya kuma, an kara dage shawarwarin zuwa karshen watan Yunin bana, amma duk da haka, bangarorin daban-daban sun yanke shawara cewa, kafin karshen watan Maris na bana, za a cimma wata yarjejeniyar siyasa, don share fagen shawarwarin da za su yi a nan gaba.
Bisa labarin da aka samu, an ce, idan aka iya kawar da sabani a cikin shawarwarin da aka yi na wannan karo, za a kaddamar da wata takarda game da ra'ayi daya da suka cimma a gun shawarwarin.(Bako)