Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce ministocin harkokin wajen kasashe shida masu tattauna kan batun nukiliyar kasar Iran, wato Amurka, Britaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran sun gudanar da wasu shawarwari a ranar 24 ga watan nan.
Yayin zatan tattaunawar sassan sun amince da cimma muhimmiyar nasara, ci gaban da a cewarsu ya aza tubalin cimma yarjejeniya kan batun nukiliyar kasar ta Iran. A hannu guda kuma kasar Sin ta nuna kyakkyawan fata ga makomar shawarwarin da ake yi kan batun.
Da yake karin hake game da hakan Mr. Wang ya cewa a matsayinta na muhimmiyar wakiliya a shawarwarin da ake yi kan batun nukiliyar kasar ta Iran, Sin ta tsaya kan adalci, tare da daukar matsayin shiga-tsakani, da bayar da shawara, wadda bangarorin masu ruwa da tsaki suka amince da muhimman hakan, lamarin da ya bada jagoranci mai ma'an ga shawarwarin dake gudana.
Ya ce kasar Sin ta kuma taka muhimmiyar rawa wajen kokarin da ake yin don warware wannan matsala baki daya. (Zainab)