Shugaban sashen kula da harkokin kwace damara na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Qun wanda ya halarci shawarwarin, ya bayyana cewa, ko da a wannan karo, ba a gudanar da cikakken taron kasashen shida da kasar Iran ba, amma, cikin kwanakin nan, an yi shawarwari da dama a tsakanin bangarori biyu ko bangarori daban daban da abin ya shafa, musamman ma a tsakanin Amurka da Iran. Sakamakon haka, an samu muhimmin ci gaba kan shawarwarin nukiliyar kasar Iran.
Kaza lika, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su tsayawa tsayin daka kan ka'idojin siyasa nasu, da kuma yin hadin gwiwa wajen ciyar da shawarwarin gaba, ta yadda za a iya cimma wata yarjejeniya ta karshe kan wannan batu. Haka kuma, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da sauran bangarorin da abin ya shafa domin ciyar da aikin gaba.
Bugu da kari, shugaban kasar Amurka Barack Obama da shugaban kasar Faransa Francois Hollande sun tattauna ta wayar tarho a ran 20 ga wata, inda suka yi kira ga kasar Iran da ta dauki matakai yadda ya kamata domin warware matsalolin dake cikas shawarwarin.
Fadar White House ta kasar Amurka ta fidda wata sanarwa dake nuna cewa shugabannin biyu, sun sake jaddada cewa, ana son cimma wata cikakkiyar yarjejeniya ta dogon lokaci ta hanyar fahimtar juna da gudanar da bincike ta yadda za a iya warware damuwar gamayyar kasa da kasa kan shirin nukiliya na kasar Iran. (Maryam)