A safiyar jiyan ne,sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, da takwaransa na kasar Iran Javad Zarif, suka gudanar da shawarwari har na tsawon sa'o'i 2 da rabi,wanda ya samu halartar ministan kula da harkokin makamashin Amurka Ernest Moniz, da na hukumar makamashi ta Iran Ali-Akbar Saleh, da ma sauran wakilan Turai. Daga bisani kuma, wakilan bangarorin shida su ma za su yi shawarwari a tsakanin bangarorin biyu-biyu da kuma bangarorin daban daban.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, idan komai ya gudana yadda ya kamata, ministocin harkokin wajen kasashen bangarori 6 za su shiga tattaunawar.
A matsayin shawarwari karo na 5, baya ga bangarorin daban daban da ke da ra'ayi guda game da dage shawarwarin, ana ganin cewa shawarwarin na wannan karo sun zamanto wani taro mai muhimmanci.
Yayin da wani babban jami'in diplomasiyya dake halartar shawarwarin ke zantawa da wakilinmu, ya ce, yanzu abubuwan da ke janyo ka-ce-na-ce cikin shawarwarin su ne, yadda za a tabbatar da hakkin Iran wajen yin amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya, da yadda kasashen duniya za su amince da Iran, a fannin raya makamashin nukiliya domin bunkasa ayyukan zaman lafiya kadai.(Bako)