Jagoran tawagar kasar Sin a taron, kana shugaban sashen hana yaduwar makamai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Qun ya ce, an gudanar da shawarwarin yadda ya kamata, tare da samun sakamako mai gamsuwa da dama, amma ya kamata bangarorin da abin ya shafa su ci gaba da aiwatar da abubuwan da suka cimma yadda ya kamata, warware sabanin dake tsakaninsu, tsai da kudurin siyasa cikin sauri. Haka kuma, kasar Sin na fatan dabaru da shirye-shiryen da ta gabatar domin warware manyan matsalolin nukiliyar kasar Iran za su taimaka ga bangarorin da abin ya shafa wajen cimma cikakkiyar yarjejeniyar da za ta dace da moriyar juna cikin sauri. (Maryam)