Kwamitin sulhun MDDr ya gudanar da wani taro a wannan rana, inda aka duba rahoton aiki na kwamitin kula da sabawa ka'idojin takunkumin kasar ta Iran. A gun taron, Wang Min ya bayyana cewa, ra'ayin kasar Sin shi ne, yanzu haka an shiga muhimmin lokaci game da shawarwarin. Kuma ya kamata bangarori daban daban su rungumi damar dake akwai, tare da ci gaba da kokarin cimma daidaito da juna.
Kazalika Wang Min ya bayyana cewa, kasar Sin na goyon bayan manufar hukumar makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA, don gane da ci gaba da taka muhimmiyar rawa, wajen warware batun nukiliyar kasar ta Iran. Har wa yau Sin na fatan kara hadin gwiwa tare da kasar Iran, domin warware matsalolin dake akwai daki-daki.
Bugu da kari a matsayinta na daya daga masu gudanar da shawarwari game da wannan batu, Sin za ta ci gaba da bada gudummawa wajen sa kaimi ga warware matsalar cikin adalci. Kana za ta ci gaba da kokari tare da bangarori daban daban, don samun nasarar warware batun nukiliyar kasar ta Iran yadda ya kamata. (Zainab)