Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na jamhuriyar musulunci ta kasar Iran ya bayar, an ce, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Marziyeh Afkham ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, kamfanin dillancin labaru na AP ya bayar da wani labari a ranar 2 ga wata, inda aka bayyana cewa, Iran da Amurka sun cimma yarjejeniya tare da amincewa da kai wasu sinadarin Uranium zuwa kasar Rasha, Afkham ta ce wannan labari ba gaskiya ba ne. Bangarori daban daban da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa ba su cimma wata yarjejeniya game da nukiliar kasar ba tukuna.
Hakazalika kuma Afkham ta bayyana cewa, watakila wannan labari na da wata manufa ta siyasa, da nufin kawo illa ga yanayin yin shawarwari a yanzu da kawo cikas ga shawarwari na gaba. (Zainab)