in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Burtaniya sun ce ba za a karawa Iran takunkumi ba
2015-01-17 17:12:28 cri
Shugaba Barack Obama na Amurka, Firaministan Birtaniya David Cameron, sun ce ba za a kakaba wa kasar Iran karin takunkumi ba, musamman a wannan gaba da ake gudanar da shawarwari kan batun nukiliyar kasar.

Shugabannin biyu sun bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labaru da suka gabatar tare, jim kadan da kammala ganawa a fadar White House a jiya Jumma'a.

Da yake tsokaci game da wannan batu Obama ya ce a halin yanzu, ana sa ran samun sakamako mai kyau, daga shawarwarin da ake gudanarwa, wanda zai iya kaiwa ga samun amincewar kasar Iran game da manufar gudanar da bincike kan harkokin nukiliyarta.

Sai dai a cewarsa kakabawa kasar karin takunkumi zai haifar da babbar illa ga hadin gwiwar gamayyar kasashen duniya a yayin shawarwarin, matakin da kuma ka iya dakile yunkurin da ake yi na warware matsalar nukiliyar kasar ta Iran ta hanyar diflomasiyya.

Har wa yau shugaba Obama, ya jaddada cewa, ba zai sa hannu kan daftarin karawa kasar Iran din takunkumi, da majalisar dokokin kasarsa ta gabatar masa ba.

A nasa bangare David Cameron, cewa ya yi Birtaniya na da niyyar dakatar da yunkurin kasar Iran na mallakar makaman nukiliya, kuma hanyar da ta dace a cimma wannan buri ita ce, dukufa wajen cimma nasarar shawarwarin da ake gudanarwa a wannan fanni, wanda hakan ne ya sa, bai dace a ci gaba da kakabawa Iran din takunkumi ba, domin a cewarsa hakan zai kara haifar da illa ne kawai ga wannan manufa, ya kuma haddasa koma baya ga hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China