in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sami babban ci gaba a yayin shawarwari kan batun nukiliya na kasar Iran duk da sabanin ra'ayi da ake fuskanta
2015-03-22 16:48:38 cri
A jiya Asabar 21 ga wata, ministocin harkokin waje na kasashen Birtaniya, Amurka, Faransa, da kuma Jamus, da babban wakilin kungiyar EU kan manufofin diplomasiyya da tsaro sun yi taro a birnin London, inda suka yi shawarwari kan yanayin da ake ciki na yin shawarwari kan batun nukiliya na Iran. Bayan taron, an ba da sanarwar cewa, an riga an sami babban ci gaba, duk da cewar har yanzu ana samun bambance-bambance a wasu fannoni.

Ministan harkokin wajen Birtaniya, Philip Hammond, da sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, da ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, da takwaran aikinsa na Jamus, Frank-Walter Steinmeier, da babbar wakiliyar kungiyar EU kan manufofin diplomasiyya da tsaro Federica Mogherini sun halarci wannan taro.

An labarta cewa, a wannan ranar, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa, za a cimma matsaya a dukkan fannoni kan batun nukiliya na kasar nan ba da dadewa ba. Amma kafin haka, dole ne Amurka ta yanke muhimmiyar shawara.

A ranar 20 ga wata, an rufe taron shawarwari kan cimma cikakkiyar yarjejeniya game da batun nukilya na Iran sakanin kasashe shida da wannan batu ya shafa a birnin Lausanne na Switzerland tare da Iran, amma ba tare da cimma kowace yarjejeniya ba. An labarta cewa, watakila za a sake komawa teburin shawarwari a karshen makon gobe.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China