Kerry wanda ya bayyana hakan a daren ranar Asabar a birnin Kabul na kasar ta Afghanistan, ya kara da cewa an amince hukumar zaben kasar ta gudanar da bincike kan dukkanin kuri'un ne karkashin sa idon jami'an tawagar MDD.
Rahotanni sun ce bayan ganawarsa da 'yan takarar biyu, Mr. Kerry ya bayyana cewa, bisa shirin da aka yi, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa dake kasar, da sojojin gwamnati ne za su yi rakiyar akwatunan zaben daga wurare daban daban zuwa birnin Kabul, sa'annan kuma a fara bincike kan kuri'un cikin awoyi 24.
Tun da fari dai hukumar zaben kasar ta Afghanistan, ta gabatar da sakamakon zaben shugaban kasar zagayen biyu ne a ranar 7 ga wata, inda aka bayyana sunan Ghani a matsayin wanda ya samu rinjaye da kaso 56.4 cikin dari na dukkanin kuri'un, yayin da kuma Abdullah ya samu kaso 43.6 cikin dari. Sai dai hukumar ta bayyana cewa an tabka magudi a yayin zagayen zaben na biyu. (Zainab)