in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ashraf Ghani ya zama sabon shugaban kasar Afghanistan
2014-09-22 10:58:09 cri

Hukumar zaben kasar Afghanistan ta gabatar da sakamakon zaben shugaban kasar a ranar lahadin nan 21 ga wata, inda ta bayyana tsohon ministan kudi na kasar Ashraf Ghani da lashe zaben, abin da ya sa ya zama sabon shugaban kasar. Wannan ya bayyana cewa, an samu nasarar mika iko karo na farko a kasar bayan da aka fara sake gina ta.

Shugaban hukumar zaben kasar Ahmad Yusuf Nuristani ya bayyana a gun taron manema labaru a wannan rana cewa, bisa sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar ta kidaya kuri'u ta bayar, da yadda 'yan takara biyu masu halartar zaben suka cimma daidaito, an sanar da cewa, Ashraf Ghani ya zama sabon shugaban kasar. Amma ba a bayyana yawan kuri'un da 'yan takaran biyu suka samu a zaben ba.

Kafin wannan, 'yan takaran biyu Ashraf Ghani da Abdullah Abdullah sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa a kasar.

Game da haka, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa ta bakin kakakinsa a ranar 21 ga wata, inda ya yi maraba da kawo karshen zaben shugaban kasar Afghanistan, kuma ya taya Ashraf Ghani murna game da zama sabon shugaban kasar.

Sanarwar ta bayyana cewa, yadda 'yan takaran biyu masu halartar zaben shugaban kasar Afghanistan suka daddale yarjejeniya game da kafa gwamnatin hadin gwiwa da yadda hukumar zaben kasar ta gabatar da sakamakon zaben, sun zama abubuwan da za su taimakawa samun zaman lafiya da wadata a kasar.

A game da wannan zabe Babban Magatakardar MDD Ban Ki-moon ya lura da cewa, sabuwar gwamnatin kasar za ta fuskanci kalubale, a don haka ya kalubalanci sabon shugaban kasar Ashraf Ghani da babban abokin takarar sa Abdullah Abdullah da ma dukkan kungiyoyin siyasa na kasar da su kafa gwamnatin hadin gwiwar kasar cikin hanzari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China