in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 2500 sun bace sakamakon bala'in zabtarewar kasa a Afghanistan
2014-05-03 16:46:21 cri
An samu zabtarewar kasa a jihar Badakhshan dake kudancin kasar Afghanistan a ran 2 ga wata, tawagar ba da tallafin jin kai ta MDD dake Afghanistan ta ba da sanarwa cewa, ya zuwa yanzu, mutane 350 suka mutu a yayin da hukumonin jihar suke sheda cewa, mutane a kalla 2500 suka bace ba a san inda suke ba.

Kafar yada labaru ta gwamnatin kasar ta ba da labarin cewa, a ran 2 ga wata da misali karfe 11 na rana, wannan bala'in ya abku a wani kauyen dake jihar Badakhshan sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya rika yi kwanakin nan, al'amarin da ya janyo lalacewar gidaje 300. Mataimakin shugaban jihar Badakhshan ya bayyana cewa, zabtarewa da aka yi har sau biyu a jere cikin awa daya a wannan rana, ta rutsa da wannan kauye, lamarin da ya lalata gidaje da dama, gangarar baraguzan duwatsu ta shafi mutane kimanin 400, kuma har yanzu ba a san ko suna raye ko a'a ba. Bala'in zabtarewar kasa na farko, ya faru a yayin da yawancin mutane suke sallar Jumma'a a wani masallaci, ta biyun kuma ta rutsa da wadanda suka zo aikin ceto. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China