MDD ta bayyana cewa, saboda akwai yiwuwar sake abkuwar zabtarewa kasa a wurin, ya sanya aka kaurar da mutane fiye da 4000 cikin gaggawa.
Kakakin jihar Naweed Forotan ya bayyana cewa, dan awa'o'i kafin an gamu da wannan babban bala'i, kauyen Aab Barik ya ci karo da zabtarewar kasa da bata da karfi. Sai dai yayin da 'yan kauye suna kokarin gano dukiya da dabbobinsu cikin baraguzan gidajensu, ba zato ba tsamani, wani dutse dake dab da kauye ya yi zabtarewa, gangarar baraguzan duwatsu ya shafi gidaje da dama.
Naweed Forotan ya ce, kididdiga ta nanu cewa, mutane fiye da 2100 suka bace cikin baraguzan duwatsu. Ta la'akari da girman duwatsu, ya sa ake tsammanin cewa ba zai yiwu ba a gano masu rai daga cikinsu. Ofishin kula da aikin jin kai na MDD ya nuna cewa, za a gabatar da hakikanin adadin hasarar rayuka ko raunuka a nan gaba. (Amina)