Cikin wata sanarwa da aka fitar, Mr. Ban ya jinjinawa kwazon al'ummar kasar ta Afghanistan, wadan da ya ce sun kada kuri'u cikin himma, lamarin da ke nuna aniyarsu ta gina makoman kasarsu yadda ya kamata, da kuma kawar da tashe-tashen hankula.
Mr. Ban ya kuma jaddada cewa, ya zama wajibi ga hukumar dake lura da babban zaben kasar, ta kidaya kuri'un da aka kada yayin zaben bisa adalci kuma ba tare da wani jinkiri ba.
Kaza lika, Mr. Ban ya bukaci 'yan takarar babban zaben kasar da magoya bayansu, da su mutunta, tare da baiwa hukuma mai lura da zaben goyon bayan da ya wajaba. Ya ce, cikin 'yan makwanni masu zuwa, ana fatan wanzuwar yanayin hadin gwiwa da farin ciki tsakanin al'ummun kasar, game da babban zaben da ya gabata. (Maryam)