Masu sa ido kan yadda zaben ya gudana, su kimanin dubu 250 ne suka ganewa idanunsu kada kuri'un, domin kaucewa magudi da karya ka'idar zaben.
Bayan kammalar kada kuri'un, babban jami'i mai kula da harkokin zaben ya bayyana gamsuwa, game da aikin kiyaye tsaro. Ya ce jami'an da suka gudanar da wannan aiki sun cancanci yabo.
Bisa tsarin mulkin kasar ta Afganistan, shugaban kasar mai ci Hamid Karzai, ba shi da ikon shiga babban zaben da aka kammala, kasancewar sa ya riga kammala zangon mulki biyu. Wannan ne dai karo na farko da za a mika mulki ga sabuwar zababbiyar gwamnatin dimokaradiyya a kasar Afganistan, tun bayan zaben farko a shekarar 2001.
Ana zaton za a kammala aikin kididdigar kuri'un babban zaben kasar a ranar 20 ga wata, za a kuma gabatar da sakamakon kafin ranar 14 ga watan Mayu mai zuwa.
Dangane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya ce, kasar Sin ta girmama zaben da jama'ar kasar Afghanistan suka kada, kuma tana fatan sakamakon babban zaben, zai haifar da ci gaba, da hadin kan jama'ar kasar, tare da inganta zaman lafiya da lumana a kasar.
Mr. Hong ya kara da cewa, ana fatan bangarorin kasar daban daban, za su kai ga warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar shawarwari, ta yadda za a iya samun fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma gaggauta farfado da zaman lafiya cikin sauri.
A wani ci gaban kuma, kwamitin tsaron MDD ya yi maraba, da yadda babban zaben kasar ta Afganistan ya gudana, tare da Allah wadai, da dukkanin wasu matakai, da ka iya yin barazana ga zabubbukan kasar ta Afghanistan. (Maryam)