Bayan karbar mulki a bainal jama'a sama da 1400 da suka kunshi al'ummar kasar da baki 'yan kasashen waje a fadar Shugaban kasar cikin tsatsauran matakan tsaro, shugaba Ashraf Ghani Ahmadzai a aikin shi na farko ya kirkiro da mukamin babban jami'i wanda ya zo daidai da firaminista a sabuwar gwamnatin na Hadaka sannan a nan take ya rantsar da Abdullah Abdullah a matsayin wannan babban jami'a a sabuwar gwamnati.
A jawabinsa na farko ga al'ummar kasar a matsayin shi na shugaban kasar, Ashraf Ghani Ahmadzai ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa, sannan ya ce zai kawo sauye sauye tare da tabbatar da mulki nagari, zai yi kokarin gudanar ayyukan yaki da talauci sannan zai bi duk hanyar da ya kamata wajen ganin rayuwar al'ummar kasar ya inganta.