Wakilin sakatare janar na MDD game da yammacin Afrika kuma babban wakilin MDD a Najeriya, Mohammed Ibn Chambas ya yi wannan alkawari a Sokoto, birnin dake arewacin Najeriya, a yayin wata ganawa tare da gwamna Aliyu Wamakko.
MDD, kamar gamayyar kasa da kasa, ta nuna damuwa game da harin baya bayan nan a garin Baga dake Borno. Wannan babban laifin keta hakkin bil'adama ne kuma ya zama wajibi a kawar da mayakan kungiyar Boko Haram, in ji Mohammed Ibn Chambas.
A game da zabuka, mista Chambas ya yi kiran 'yan Najeriya da su kiyaye daukar ranakun zabe a matsayin wasu ranaku na tashin hankali.
Najeriya na da babban matsayin da za ta dauka a Afrika da duniya, kuma dukkan hankali ya karkata yanzu kan wannan kasa domin ganin an shirya zabukan gaskiya da sahihanci, cikin adalci da kowa zai amince, in ji wannan jami'in.
Haka kuma, mista Chambas ya kuma gayyaci hukumomin tsaro da su samar da wani yanayi mai kyau da zai taimakawa 'yan Najeriya zaben 'yan takarar da suke so, ba tare da matsin lamba ko nuna karfin tuwo. Ya kamata shugabanni su rika isar da sako na kwarai ga magoya bayansu game da 'yancin zaben wanda suke so a yayin zabuka. (Maman Ada)