Babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon, ya bukaci gudanar da babban zaben Najeriya, bisa sabon jadawalin da aka bayyana, yana mai fatan zaben zai gudana ba tare da wata matsala ba.
Cikin wata sanarwar da kakakinsa ya fitar, Mr. Ban ya bayyana gamsuwa game da shirin da hukumar gudanar da zaben kasar mai zaman kanta ta yi, a fannin raba katunan zabe ga al'ummar kasar, ya na mai kira ga hukumomin kasar masu ruwa da tsaki game da zaben, da su tabbatar dukkanin jama'ar kasar sun samu damar kada kuri'un su cikin 'yanci, ba kuma tare da fuskantar ko wace irin barazana ba.
Dadin dadawa, Mr Ban ya ce MDD na maida hankali kwarai kan tashe-tashen hankula masu alaka da zabe, don haka ya ja hankalin shugabannin daukacin jam'iyyun siyasar kasar, da su cika alkawarinsu na kaucewa rura wutar rikici, su kuma nuna rashin amincewa da kalaman mabiyansu, wadanda ka iya tada husuma ko haifar da cikas ga zaben dake tafe. (Amina)