Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nigeriya tace ta raba katunan zabe na din din din miliyan 52.23 a daukacin fadin kasar, wato kimanin kashi 75.88 a cikin 100 na adadin masu zabe da aka yiwa rijista.
Kakakin hukumar Kayode Idowu ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da Xinhua ta samu.
Tunda farko sai da mai bada shawara a harkan tsaron kasar Sambo Dasuki ya bukaci hukumar zaben da ta jinkirta gudanar da zaben na ranar 14 ga wata domin kara bada lokacin da al'umma zasu sami karban katunan zaben su.
Sambo Dasuki yace an raba katunan fiye da miliyan 30 a shekarar data gabata sannan kusan wannan adadin na jiran karban nasu.
Wannan zabe dai shi ne na farko da ake bukatar masu jefa kuri'a su mallaki katunan zaben na amfanin da na'ura.