in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
INEC ta ce za ta sanar da sakamakon zabukan kasar bayan sa'o'i 48
2015-02-16 11:16:39 cri

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta (INEC) ta ce, za ta sanar da sakamakon zabukan kasar sa'o'i 48 bayan kammala kada kuri'u.

Kwamishina a hukumar Amina Zakari wadda ta bayyana hakan a jihar Kebbi da ke arewacin kasar ta Najeriya yayin wani taron ilimantar da jama'a game da yadda ake tantance masu zabe da tafiyar da harkokin zaben ta ce, sabon tsarin zabukan na shekara 2015 zai tabbatar da gaskiya da adalci.

A cewarta, an shirya taron ne don baiwa jami'an zabe damar fahimtar tsarin tantance masu kada kuri'a ta yadda zaben zai gudana cikin lumana.

Don haka ta yi kira ga masu kada kuri'a, da su kasance cikin layi a kan lokaci domin a tantance su, tana mai ta ba tabbacin cewa, za a tattara alkaluma yadda ya kamata bayan kammala zabe.

Hajiya Zakari ta kara da cewa, canjin ranar zaben ya baiwa hukumar kara kimtsawa sosai. Ta kuma yi alkawarin cewa, za a samar da isassun jami'an tsaro a dukkan matakan zabukan.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China