in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun gano wasu dimbin muggan makamai  mallakar 'yan ta'adda
2015-02-02 14:42:44 cri
Jiya Lahadi ranar 1 ga wata, babbar hedkwatar tsaro ta sojojin Najeriya ta ce, a yanzu haka dakarun Najeriya dake arewa maso gabashin kasar sun cafke wasu dimbin makamai mallakar 'yan kungiyar Boko Haram a yayin da suka fatattaki 'yan kungiyar.

Kakakin hedkwatar tsaron Manjo Janar Chris Olukolade ya fada cewa, sojojin Najeriya sun kame makamai da albarusai, ciki har da wasu motocin sulke 2, da bindigogin atilari 2 da motoci 17 kirar hilux a wasu wurare daban daban a jihar Borno a yayin da suka zafafa kaimin ayyukansu.

Olukolade ya ce, yanzu haka aka sanya matakan tsaro a wuraren da sojojin suka ceto daga hannun 'yan ta'adda, kuma sojojin da suka sami rauni ana ci gaba da duba lafiyarsu. Kana kamar yadda ya ce, ana ci gaba da farautar 'yan ta'addan wadanda suka gudu a halin yanzu saboda farmakin da ake ci gaba da kai masu. Kakakin sojojin na Najeriya ya kara da cewa, aikin da suke gudanarwa suna yin shi ne tare da hadin kan sojojin kasashen duniya.

Olukolade ya ce, sojojin sun samu nasarar dakatar da harin 'yan boko haram a Maiduguri. Bugu da kari, ya furta cewa, 'yan ta'addan za su fuskanci hari ta ko wace fuska musamman daga bangare dakarun kasashen Chadi, Kamaru, Jamhuriyar Nijar da kuma Nijeriya. Kuma ana sa ran samun nasara a kan 'yan ta'addan masu tada zaune tsaye.(Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China