A cewar kakakin MDDr Stephen Dujarric, uwargida Zerrougui ta bayyana hakan ne bayan kammala ziyararta a Najeriya, inda ta ganewa idanunta illar da tashe-tashen hankula ke wa yara kanana a yankin na Arewa maso Gabashin kasar.
Dujjaric ya rawaito uwargida Zerrougui na bayyana takaicin yadda 'yan mata a wannan yanki ke fuskantar cin zarafi da ya hada da fyade da kuma auren dole. Ta ce cikin shekarar 2014 da ta gabata, an samu karuwar ayyukan tada kayar baya, da shigar da yara kanana cikin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi, da yin garkuwa da yara, da kuma kaiwa makarantu hare-hare.
Zerrougui ta bada misali da harin bam da wata yarinya mai shekaru 10 ta kai wata kasuwa dake birnin Maiduguri, harin da ya hallaka mutane 20 a matsayin abin takaici, dake nuna karuwar amfani da yara kanana a harin kunar bakin wake. Ta ce sace 'yan matan Chibok su 270 da kungiyar Boko Haram ta yi, da kuma da'awar da shugaban kungiyar ya yi na sayar da 'yan matan wani abu ne mai matukar sosa rai.
Kalaman jami'ar MDD dai na zuwa ne, yayin da Najeriyar ke ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro, musamman ma daga kungiyar Boko Haram mai da'awar yunkurin kafa daular Islama a kasar. (Saminu Alhassan)