in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi aikin gwajin allurar maganin Ebola a Guinea
2015-03-06 14:55:25 cri

Jiya Alhamis 5 ga wata, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gabatar da wata allurar maganin cutar Ebola samfurin VSV-EBOV, wadda kasar Canada ta kirkiro, allurar da ake fatan yin gwajinta a kasar Guinea, daga ranar 7 ga wannan wata na Maris da muke ciki. An ce za a yi amfani da allurar a wurare daban-daban da zarar an samun nasarar gwajin da za a yi.

WHO ta nuna cewa, za a yi aikin gwajin ne a yankin Basse Guinee, inda cutar ta fi adabbar al'umma. Kuma hanyar da za a bi ita ce, mai da hankali kan wani mutumin da aka tabbatar ya kamu da cutar Ebola, da mutanen dake da alaka da shi, daga baya za a yi allurar ga dukkanin wadannan mutane, kamar da yadda aka yi ga cutar agana a karnin da ya gabata.

Ban da haka kuma, za a samarwa masu aikin jiyya dake wurin irin wannan allura.

Babbar daraktar hukumar WHO Madam Dr Margaret Chan ta ce, idan an tabbatar da amfanin wannan allura, za ta zama matakin farko daka iya hana yaduwar cutar Ebola a duniya.

Dadin dadawa, WHO ta fitar da wani rahoto dake cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar ya ragu sosai a 'yan kwanakin nan. Wanda hakan ke nuna cewa an kusan cimma burin kawo karshen cutar, gabanin wa'adin ranar 15 ga watan Afrilu, kafin fara aikin share fagen farfado da wurare da cutar ta fi adabba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China