in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta jinjinawa Sin bisa kokarin tallafawa kasashen da suka sha fama da Ebola
2015-03-03 09:40:16 cri

Mai magana da yawun shirin gaggawa domin yaki da cutar Ebola na MDD Fatoumata Lejeune-Kaba ta jinjinawa kokarin da kasar Sin ta yi wajen baiwa kasashen da suka fi fama da cutar Ebola tallafin shawo kan cutar.

Lejeune-Kaba ta bayyana amannarta da tallafin na Sin, lokacin da take zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, tana mai cewa, baya ga taimakon kayan da ake bukata wajen yaki da cutar, Sin ta kuma ba da gudummawar likitoci da kwararru da ma'aikatan jiyya.

Ta ce, bisa jimilla, darajar taimakon da Sin ta bayar ya tasamma dalar Amurka miliyan 120, bacin dala miliyan 10 da ta baiwa kungiyoyin ba da agajin jin kai na kasa da kasa a matsayin karin tallafi.

Wakiliyar ta MDD ta kara da cewa, mahukuntan Sin sun yi aiki kafada da kafada da kasashen nan uku da cutar Ebola ta fi kamari, wajen gudanar da ayyuka, da gina wuraren kula da wadanda suka kamu da cutar a matakai daban daban.

Daga nan sai ta yi fatan kasar ta Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashen Guinea, da Liberia da Saliyo, wajen inganta shirinsu na ganin bayan cutar Ebola kaco kan.

Kididdigar baya bayan nan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar, ta nuna cewa, Ebola ta hallaka kusan mutane 9000 a wannan karo. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China