Wakilin musamman na MDD game da yaki da cutar Ebola David Nabarro, ya ce ya zama wajibi a kara zage damtse, wajen ganin an kabbabe ragowar cutar Ebola, daga kasashen nan 3 na yammacin Afirka.
Nabarro wanda ya shaidawa mahalarta zaman MDDr hakan a jiya Laraba, ya ce duk da nasarar da ake samu game da yaki da cutar, a hannu guda akwai bukatar kara kwazo matuka, ta yadda za a iya kaiwa ga ganin bayan ta kacokan.
Ya ce a halin da ake ciki ana dada maida hankali ga aikin sa ido, domin gano ragowar masu dauke da cutar, da wadanda suka yi mu'amala da su, tare da lura da irin wannan aji na al'umma har tsahon makwanni 3, aikin da ya bayyana a matsayin mai matukar wuyar gaske.
A nasa jawabi, babban magatakardar MDDr Ban Ki-moon, cewa ya yi yanayin yaduwar Ebola ya sauya, kuma koda yake masu kamuwa da cutar sun yi matukar raguwa, a daya hannu ana samun sabbin masu harbuwa da ita a Guinea da Saliyo.
Mr. Ban yace hakan ya shaida cewa ana iya samun koma baya, bayan nasarorin da ake ganin an cimma, don haka ya jaddada bukatar kara sanya ido da lura, har a yankunan da a baya ba a samu bullar cutar ba.
Alkaluman kididdiga sun nuna cewa kusan mutane 23,000 ne suka kamu da cutar Ebola a wannan karo, kuma tuni ta hallaka sama da mutane 9,200.