Cibiyar nazarin ta ce tun daga ranar 17 ga watan Disambar bara, tare da wasu kungiyoyin likitoci sun kafa cibiyoyin bada jinya ga wadanda suka harbu da cutar Ebola 4 a kasar Guinea, kana sun yi gwajin maganin na Avigan(favipiravir) ga mutane 80 da suka kamu da cutar ta Ebola.
Bisa sakamakon da aka samu, an ce Avigan(favipiravir) ya yi amfani matuka, wajen rage yawan mutuwar mutanen da suka kamu da cutar, daga kashi 30 cikin dari zuwa kashi 15 cikin dari. (Zainab)