A jiya Talata ne dai aka gudanar da taron, karkashin hadin gwiwar kungiyar EU, da kasar Liberia, da Saliyo, da Guinea, da kungiyar AU, da kungiyar ECOWAS, da kuma MDD a birnin Brusels na kasar Belgium.
Cikin jawabin da ya gabatar ministan harkokin wajen kasar Saliyo Samura Kamara, ya ce kasar Sin kasa ce ta farko dake taimakawa kasar Saliyo wajen yaki da cutar Ebola. Kuma ya zuwa yanzu Sin ta riga ta samar da gudummawa har karo hudu ga kasar Saliyo, ciki har da tallafin kudi, da na'urorin kiwon lafiya, da motoci, da likitoci da dai sauransu.
Shi kuwa babban jami'in hukumar zartaswa ta kwamitin tallafin bala'in fari na Oxford dake Birtaniya Mark Goldring, cewa ya yi kasashe 3 na yammacin Afirka da cutar tafi shafa suna kokarin amfani da taimakon da kasashen duniya ke basu. Kuma kasar Sin da kasashen uku za su iya yin hadin gwiwa, wajen tsara shiri game da yadda za a bunkasa fannonin kiwon lafiya, da bada ilimi, da harkokin aikin gona, da tattalin arziki da dai sauransu, kana da batun yin amfani da tallafin da suke samu yadda ya kamata. (Zainab)