Yan majalisun gamayyar tattalin arzikin yammacin Afrika (ECOWAS) sun kaddamar a ranar Talata a birnin Dakar na kasar Senegal da tattaunawa domin bullo da hanyoyi da matakan shiga yaki domin kawar da cutar Ebola dake ci gaba da yin ta'adi a cikin kasashe uku mambobin kungiyar wadanda suka hada da Guinea, Saliyo da Liberiya.
A tsawon kwanaki biyar, taron zai mai da hankali kan "annobar cutar Ebola, sauyin da aka samu, da sakamakon da aka cimma wajen cutar, da kuma abubuwan da za'a yi a nan gaba." Taron na gudana a karkashin jagorancin kwamitin hadin gwiwa na ECOWAS dake kunshe da kwamitin kiwon lafiya da ma'aikatun jama'a da kwamitin dake kula da mata, aiki da jin dadin jama'a.
A yayin bikin bude taron, 'dan majalisar kasar Senegal, Moustapha Cisse Lo, kuma wakilin shugaban majalisar dokokin kungiyar ECOWAS, ya bayyana cewa, mahalarta taron za su yin nazari kan illolin wannan cuta kan tattalin arziki, jama'a da siyasa, da kuma gabatar da matakan da za su zo su aza kan wadanda tuni gamayyar kasa da kasa da shiyyar yammacin Afrika suka tsara. (Maman Ada)