Hukumomin kasar Guinea tare da taimakon abokan huldarsu a fannin kiwon lafiya, da suka hada da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), kungiyar likitoci (MSF) da kuma CDC Atlanta wato cibiyar shawo kan cututtuka sun dauki matakin kawo karshen cutar Ebola a cikin kwanaki 60 wato zuwa karshe a ranar 10 ga watan Maris mai zuwa.
Domin kai ga suman nasara game da wannan babban mataki, ganin yadda wannan cuta ke kamari a wasu yankuna kamar yankin Kindia dake Basse Guinea, inda sanya ido kan jama'a, da ma wasu mutanen da suka kamu da cutar Ebola ke kasancewa har yanzu wata babbar matsala, dalilin matakin nuna himmatuwa daga dukkan fannoni.
Daga wajen bangaren, ma'aikatan kiwon lafiya zuwa shugabannin al'ummomi, shugabannin addinai, tare da kwamitocin jama'a na kauyuka, kawo na da aikin da aka dora masa domin samun nasara kan wannan annoba.
Wani binciken da aka fitar a wannan ranar 23 ga watan Febrairu ya nuna cewa, an samu sabbin mutanen da suka kamu da Ebola guda 24 a fadin kasar tun daga ranar 20 ga watan Janairu, inda aka samu 4 a Conakry, 1 a Dubreka, 8 a Forecariah, 8 a Coyah, 1 a Kindia, 1 a Lola, 1 a Mali tare kuma da mutuwar mutane 11. Daga cikin wadannan yankuna, biyar sun fito daga yankin Basse Guinea, kana biyun tsakanin Moyenne Guinea da Guinea Forestiere. Baki daya, alkaluma sun nuna cewa, mutane 2758 aka tabbatar da kamuwa da cutar Ebola, daga cikinsu 1699 sun mutu. (Maman Ada)