in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Akwai bukatar yin taka-tsantsan game da hangen nasarar da ake samu a yaki da cutar Ebola a Liberiya
2015-02-20 16:30:33 cri

Shugaban tawagar yaki da cutar Ebola ta MDD Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya ja hankalin mahukunta da al'ummar kasar Liberiya, game da hadarin da kasar ke fuskanta don gane da yaduwar cutar Ebola duk da nasarar da aka samu.

Jagoran tawagar ta UNMEER wanda ke gudanar da nazari a karo na biyu, game da yaduwar cutar a kasashen yammmacin Afirkan nan 3 da cutar ta fi kamari, ya ce ya zuwa yanzu Liberia bata kai ga cika sharuddan da hukumar lafiya ta WHO ta gindaya na kawo karshen cutar ba.

Ahmed ya ce duk da haka, mahukuntan ta, da sauran hukumomin da abun ya shafa, sun yi namijin kokari wajen aiwatar da manufofin da suka taimaka matuka ga yakin da ake yi da cutar.

Ya ce babbar manufar yaki da cutar Ebola itace tabbatar da dakatar da yaduwar ta kacokan, don haka ake da bukatar hadin kan dukkanin masu ruwa da tsaki wajen cimma wannan buri.

Kaza lika Ahmed ya lasafta batun inganta harkokin kiwon lafiya, da aiwatar da matakan kandagarki, tare da dukkanin wasu manufofi na kula da lafiyar al'umma, a matsayin hanyoyin da ya dace a bi domin dakile sake yaduwar cutar Ebola a kasar ta Liberia.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China