Bankin duniya zai yi hadin gwiwa da shirin samar da abinci da aikin gona( FAO) gami da hukumomin kasar Guinea wajen samar da dala miliyan 5 don tallafawa al'ummomin da ke matukar bukatar agaji a yankunan karkarar kasar Guinea.
Kakakin MDD Farhan Haq wanda ya bayyana hakan jiya yayin taron manema labarai da aka saba yi ya ce, za a horas da dubban al'ummomin da ke yankunan karkarar kasar Guinea da cutar Ebola ta shafa ne game da hana yaduwar cututtuka da hanyoyin noma abinci da samun kudaden shiga.
Kakakin na MDD ya ce,iyalai 30,000 ne za su amfana da wannan shiri na samun horo kan yaki da yaduwar cututtuka a yankunan karkara,inda kwararrun ma'aikata a fannin raya yankunan karkara za su gudanar da ayyukan ilimantar da jama'a tare kuma da raba musu kayayyakin tsaftace muhalli.(Ibrahim)