in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika da EU na tattaunawa domin maido hulda bayan barkewar Ebola
2015-02-27 10:45:33 cri

Kungiyar tarayyar Turai (EU) ta gayyaci kasashen Afrika a wani babban zaman taro na manyan jam'ai a birnin Brussels wanda ke da manufar sake duba kokarin da ake yanzu haka wajen yakin da ake yi da cutar Ebola, tare da kuma kafa wani shirin taimakawa Liberiya da sauran kasashen Afrika, ta yadda za su farfado daga illar wannan annoba.

A cikin wata sanarwar kungiyar EU, da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kofi a ranar Alhamis, ta nuna cewa, shugabanni da ministocin Guinea, Saliyo da Togo, da ma wakilan kwamitin tarayyar Afrika (AU), MMD, kungiyar ECOWAS da tarayyar Turai (EU) za su halarci taron manyan jami'ai.

Shugabar Liberiya, Ellen Johnson-Sirleaf, a matsayinta ta shugabar da za ta jagoranci taron kan Ebola cikin hadin gwiwa, za ta kuma gabatar da jawabi a matsayinta na kakakin kungiyar kasashen kogin Mano (MRU).

A yayin wannan zaman babban taro ne, za'a sanya hannu tsakanin Liberiya da EU kan shirin kasa na asusun ci gaba na tarayyar Turai game da kasar Liberiya na shekarar 2014 zuwa 2020 karo na 11, wanda kuma zai kasance shirin taimako mafi muhimmanci na EU ga kasar Liberiya bisa tsawon shekaru masu zuwa, in ji wannan sanarwa.

Asusun ya baiwa Liberiya dalar Amurka miliyan 326, kudaden da za'a raba su zuwa fannoni hudu da suka hada mulki na gari, makamashi, ilimi da noma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China