Shirin ya shafi shigo da dalar Amurka miliyan 45.6 ta hanyar saukaka samun rance cikin sauri da sassauta kai tsaye bashin kasar na dalar Amurka miliyan 36.5 daga asusun bada tallafi da magance bala'u daga indallahi.
Kawo saukin rance zai taimaka hukumomin kasar Liberiya yaki da annobar cutar ta hanyar biyan bukatun kudi, da biyan albashi da kuma karfafa kudin ajiya na kasa da kasa.
Haka kuma, asusun IMF ya bayyana cewa sassauta bashin Liberiya zai taimaka wajen zaburar da taimakon gamayyar kasa da kasa.
Naoyuki Shinohara, mataimakin darekta janar na IMF, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa annobar cutar Ebola na ci gaba da gurgunta tattalin arzikin Liberiya duk da raguwar mutanen da suka kamu da cutar a kasar, ya kara da cewa bukatun kudi da shigo da jarin kasashen waje sun kara karuwa fiye da yadda aka tsaida. Tattalin arzikin Liberiya zai farfado a shekarar 2015 bayan tsaikon da ya samu a shekarar 2014 dalilin annobar Ebola da faduwar jarin kamfanonin hakar ma'adinai da na ababen more rayuwa . (Maman Ada)