Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta yi maraba ga ma'aikatan kiwon lafiya kashi na farko wadanda aka tura domin yaki da cutar Ebola a kasashen da suka yi kamari.
Kungiyar ta AU ta tura ma'aikatan kiwon lafiya a karkashin shirinta na taimaka wa kasashen da ke fama da cutar Ebola a yammacin Afrika wato ASEOWA, kuma tawagarta ta farko ta dawo daga Liberiya a ranar 22 ga wannan watan bayan kammala aikinta, in ji wata sanarwa da kungiyar ta fitar a cibiyarta dake Adis Ababa na kasar Habasha.
Ma'aikatan da suka fito daga kasashen Nigeriya, Rwanda, Habasha, Uganda da jamhuriyar demokradiya ta Kongo na kunshe da likitoci, masu aikin jinya, masu aikin sadarwa da kuma guda daya mai ba da horo a kan kula da majinyancin Ebola.
Ma'aikatan tawagar dai sun samu maraba ne daga wajen shugaban kwamitin kungiyar Madam Nkosazana Dlamini Zuma a bikin da aka ce shi ne irin shi na farko da kungiyar AU ta shirya domin yin maraba ga gwazayenta da suka je yaki da cutar ta Ebola, kuma ba tare da sun kamu da cutar ba.
Madam Dlamini Zuma ta gode wa ma'aikatan kiwon lafiyan bisa ga wannan kokarin nasu, tare da tabbatar masu da cewar, kungiyar AU a shirye take ta murkushe cutar gaba daya,
Duk wadanda suka dawo, an ba su takardun karramawa bisa ga yaba musu gudumuwar da suka bayar wajen sadaukar da aniyarsu ta yaki da cutar. (Fatimah)