Hakan a cewar sanarwar da fadar gwamnatin kasar ta fitar a jiya Juma'a, ya biyo bayan shawarar da majalissar tsaron kasar ta bayar ne.
Dage wannan doka ta hana zirga-zirga dai za ta fara aiki ne tun daga ranar Lahadi 22 ga watan nan. Kaza lika gwamnatin Liberian ta amince da a sake bude kan iyakokin kasar da aka rufe. An kuma umarci ma'aikatar lafiyar kasar da ta aiwatar da tsare-tsare, da zasu tabbatar da hana bullar cutar a dukkanin sassan kasar.
A ranar 8 ga watan Satumbar bara ne dai shugaba Sirleaf ta ayyana gyaran da aka yiwa waccan doka ta hana fita, inda aka maida wa'adin aikin ta, ya zamo tsakanin karfe 12 na dare zuwa karfe 6 na safiyar kowace rana. An kuma yi amfani da ita a dukkanin sassan kasar, har ya zuwa wannan lokaci da aka bayyana dakatar da ita.