Shugaban kasar Saliyo Koroma ya jinjinawa kasar Sin a game da yadda take taimkawa kasarsa yaki da cutar Ebola mai saurin kashe jama'a.
Shugaba Koroma yana jawabi ne a yayin da darektan bangaren hulda da kasashen waje na hukumar lafiya da tsarin iyali ta kasar Sin Ren Minghui ya kai masa ziyara a fadar gwmnatin kasar dake birnin Freetown.
Shugaban kasar ta Saliyo ya yi nuni da cewar, kasar Sin kasa ce mai mutunci domin ta cika alkawarin da ta yi wa Saliyo na gina mata cibiyar binciken cututtuka na din-din-din.
A nashi jawabin, Ren Minghui ya ce, cibiyar binciken cututtukan za ta kara dankon dangantaka tsakanin kasashen 2, a inda ya bayar da shawarar amfani da asibitin Jui a matsayin wata cibiya ta binciken cututtuka da kuma daukar mataki na magance cututtukan.
Ren ya kuma ba da shawarar kara dankon dangantakar Sin da Saliyo ta yadda ma'aikatan lafiya na Saliyo za su amfana da kwarewar kasar Sin.
Darektan na kasar Sin ya kai ziyara Saliyo ne saboda kaddamar da cibiyar binciken dake kusa da asibitin da kasar Sin ta gina. (Suwaiba)